9 Maris 2016 - 17:15
Shugaban Jami'an Al-Azhar Ya Bukaci Zama Tare Da Malaman Shia Da Sunna.

Shugaban Jami'an Al-Azhar ta kasar Masar ya sake bukatar a gudanar da taro tsakanin manya manyan malaman Shia da sunna don samun hadin kai a tsakaninsu.

Kamfanin dillancin Al-qur'ani na kasa da kasa (Ekna) ya nakalto daga shadin yanar gizo na «الامة الاخباریة» tana fadar cewa Ahmad Tayyeed ya yi wannan kiran ne a jiya Talata a lokacinda yake ganawa da shugaban kasar Iraqi Fu'ad Maasum wanda yake ziyarar aiki a kasar.

Sheikh Ahmad Tayyeed ya kara da cewa akwai bukatar hadin kai tsakanin musulmi kuma malaman manya manyan mazhabobin ne yakamta su jagoranci lamarin. Sheikh Tayyeeb ya bayyana goyon bayansa ga mutanen kasar Iraqi a kokarin da suke na yaki da yan ta'adda wadanda suke son raba kan al-ummar musulmi.

Shima a na shi bangaren shugaban kasar Iraqi ya bayyana cewa kasarsa a shirye take ta haka kai da kasar Masar don cimma manufofi masu amfanar kasashen biyu.288